ILLAR MUGUNTA .
Mugunta wata cuta ce ta tunani da zuciya, da aiki ,wadda idan ta yi katutu cikin al'umma, sai ta hana zaman lafiya, ta kawo rashin fahimta, ta haifar da rikice-rikice, ta ruguza cigaba, kuma ta rushe duk wani gini na kwanciyar hankali da zaman Lafiya.
Mugunta ita ce yin wani abu da gangan wanda ke cutar da wani mutum, ko kuma ke da illa ga rayuwar al’umma. Wannan ya haɗa da halayen da suka danganci hassada, kiyayya, riƙe zuciya, yaudara, cin amana, kage, ƙiyayya, zalunci, ɓata gari, da sauransu.
Mugunta na bayyana ta fuskar tunani, kalmomi da ayyuka. Mutum mai mugunta kan yi abu ba tare da jin tausayin wasu ba, yana fifita kansa da son zuciyarsa fiye da maslahar kowa da kowa.
Ire-Iren Mugunta
1. Muguntar Zuciya: Irin su hassada, kyashi, ƙiyayya da mugun zato.
2. Muguntar Harshe: Karya, zagi, kage, ɓatanci, ɓarnar magana.
3. Muguntar Aiki: Zalunci, sata, fyade, kashe-kashe, cin hanci da rashawa.
4. Muguntar Shugabanci: Rashin adalci, cin amana, rashin gaskiya a mulki da fifita jama’a bisa bambanci.
1. Rashin Aminci da Kwanciyar Hankali
Idan mugunta ta mamaye zukata, al’umma ba za ta samu zaman lafiya ba. Wannan yana kawo rikice-rikice, rikicin ƙabilanci ko addini da fitintinu, wanda ke hana ci gaba.
2. Rushewar Tattalin Arziki
Sata, rashawa da cin hanci mugayen halaye ne da ke haifar da durƙushewar tattalin arziki. Lokacin da shugabanni suka rungumi mugunta, sai su sace dukiya, su hana al’umma ingantaccen rayuwa.
3. Lalata Matasa
Mugunta tana harfar da barna, laifuka da shaye-shaye su Kuma suna lalata matasa, su zama barazana ga zaman lafiya da amfanin su a gobe. Wannan yana dakile ci gaban ƙasa gaba ɗaya.
4. Karuwar Jahilci da Rashin Ilimi
A cikin al’umma mugunta na jawo makarantun kan durƙushe, saboda rashin tsaro ko son zuciya. Wannan na hana yara da matasa samun ilimi mai inganci, wanda shi ne ginin ci gaba.
Mugunta babban kalubale ne ga ci gaban kowace al’umma. A duk inda mugunta ta mamaye, to ci gaba yana jinkiri ko kuma ya tsaya cak. Saboda haka, akwai buƙatar kowa da kowa ya tsaya ya tsarkake zuciyarsa, ya guji mugunta da ayyukanta, domin a samu ci gaba mai ɗorewa, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin jama'a.
Allah Ya tsaremu daga mugunta da mugayan mutane.
