Unified African Muslim scholars

Islamic knowledge for a brighter tomorrow

Posts, audio, books and answered questions from the scholars you follow, in one place. Free to read and listen.

Explore the scholarsListen now

Coming soonApp Store Coming soonGoogle Play
Have an account?
New to Almuhajir?

Sign in

or
Assalamu alaikum,
You're signed in. Pick up where you left off.

Latest from the scholars

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
ILLAR MUGUNTA . Mugunta wata cuta ce ta tunani da zuciya, da aiki ,wadda idan ta yi katutu cikin al'umma, sai ta hana zaman lafiya, ta kawo rashin fahimta, ta haifar da rikice-rikice, ta ruguza cigaba, kuma ta rushe duk wani gini na kwanciyar hankali da zaman Lafiya. Mugunta ita ce yin wani abu da gangan wanda ke cutar da wani mutum, ko kuma ke da illa ga rayuwar al’umma. Wannan ya haɗa da halayen da suka danganci hassada, kiyayya, riƙe zuciya, yaudara, cin amana, kage, ƙiyayya, zalunci, ɓata gari, da sauransu. Mugunta na bayyana ta fuskar tunani, kalmomi da ayyuka. Mutum mai mugunta kan yi abu ba tare da jin tausayin wasu ba, yana fifita kansa da son zuciyarsa fiye da maslahar kowa da kowa. Ire-Iren Mugunta 1. Muguntar Zuciya: Irin su hassada, kyashi, ƙiyayya da mugun zato. 2. Muguntar Harshe: Karya, zagi, kage, ɓatanci, ɓarnar magana. 3. Muguntar Aiki: Zalunci, sata, fyade, kashe-kashe, cin hanci da rashawa. 4. Muguntar Shugabanci: Rashin adalci, cin amana, rashin gaskiya a mulki da fifita jama’a bisa bambanci. 1. Rashin Aminci da Kwanciyar Hankali Idan mugunta ta mamaye zukata, al’umma ba za ta samu zaman lafiya ba. Wannan yana kawo rikice-rikice, rikicin ƙabilanci ko addini da fitintinu, wanda ke hana ci gaba. 2. Rushewar Tattalin Arziki Sata, rashawa da cin hanci mugayen halaye ne da ke haifar da durƙushewar tattalin arziki. Lokacin da shugabanni suka rungumi mugunta, sai su sace dukiya, su hana al’umma ingantaccen rayuwa. 3. Lalata Matasa Mugunta tana harfar da barna, laifuka da shaye-shaye su Kuma suna lalata matasa, su zama barazana ga zaman lafiya da amfanin su a gobe. Wannan yana dakile ci gaban ƙasa gaba ɗaya. 4. Karuwar Jahilci da Rashin Ilimi A cikin al’umma mugunta na jawo makarantun kan durƙushe, saboda rashin tsaro ko son zuciya. Wannan na hana yara da matasa samun ilimi mai inganci, wanda shi ne ginin ci gaba. Mugunta babban kalubale ne ga ci gaban kowace al’umma. A duk inda mugunta ta mamaye, to ci gaba yana jinkiri ko kuma ya tsaya cak. Saboda haka, akwai buƙatar kowa da kowa ya tsaya ya tsarkake zuciyarsa, ya guji mugunta da ayyukanta, domin a samu ci gaba mai ɗorewa, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin jama'a. Allah Ya tsaremu daga mugunta da mugayan mutane.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
An kawata duniya da abubuwa biyar: 1. Ilimi da malamai 2. Adalcin shugabanni 3. Ibadar bayin Allah 4. Amanar ’yan kasuwa 5. Kyakkyawar nasiha daga masu ba da shawara Sai kuma Iblis ya zo da tutoci guda biyar domin ya lalata waɗannan abubuwa: * Ya zo da hassada domin ya yaƙi ilimi. * Ya zo da zalunci domin ya yaƙi adalci. * Ya zo da riya domin ya lalata ibada. * Ya zo da ha’inci domin ya lalata amana. * Ya zo da yaudara da ruɗi domin ya lalata nasiha. Darasi: Idan aka kiyaye ilimi daga hassada, adalci daga zalunci, ibada daga riya, amana daga ha’inci, da nasiha daga yaudara, al’umma za ta kasance cikin alheri da zaman lafiya. تفسير الرازي مفاتح الغيب 2/402.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
ABUBUWA GOMA DA SUKE HANA MUTUM YA YI NADAMA A RAYUWA 1. Tsoron Allah: Duk wanda yake tsoron Allah a cikin dukkan lamuransa, zai kiyaye kansa daga aikata abin da zai jawo masa nadama. 2. Yin tunani kafin magana: Kada ka yi magana kafin ka yi tunani, domin kalmar da ta fito daga bakinka ba za ta dawo ba. 3. Gaggawar yanke hukunci: Kada ka yanke hukunci cikin fushi ko damuwa, domin sau da yawa gaggawa tana haifar da nadama. 4. Tuntubar masu hikima: Ka saba neman shawarar mutanen kirki da masu basira kafin ka shiga manyan al’amura. 5. Rashin bin son zuciya: Kada ka bari sha’awarka ta rinjayi hankalinka, domin ba duk abin da kake so ne yake da amfani gare ka ba. 6. Kiyaye sirri: Kada ka bayyana dukkan sirrinka ga kowa, domin ba duk mai murmushi gare ka ne yake maka fatan alheri ba. 7. Zabar abokan kirki: Ka zaɓi abokan da za su taimake ka wajen biyayya ga Allah da kyautata rayuwarka. 8. Yafiya da kau da kai: Kada ka ɗauki duk wani abu a ranka. Ka koyi yafiya, haƙuri da kau da kai daga abubuwan da ba su cancanci damuwarka ba. 9. Godiya da wadatar zuci: Ka gode wa Allah bisa abin da yake hannunka, kada ka riƙa kwatanta rayuwarka da ta wasu. 10. Tuba da gyara kuskure: Idan ka yi kuskure, ka amince da shi, ka nemi gafarar Allah, ka gyara abin da za ka iya gyarawa, kada ka nace a kan kuskure. Rayuwa ba ta rasa kuskure, amma mai hankali shi ne wanda yake koyo daga kuskurensa kafin ya zama nadamarsa. Kada ka yanke shawara saboda fushi, kada ka yi magana saboda kwaɗayi, kada ka rasa alheri saboda girman kai, kuma kada ka manta cewa duk abin da ka aikata za ka ga sakamakonsa. Allah Ya ba mu hikimar da za mu yi rayuwa cikin imani, basira da kyakkyawan ƙarshe. آمِينَ.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
BA KOWA NE YA CANCANCI WURI A RAYUWARKA BA! Mutane kashi shida ne 1️⃣ Wani kamar rai yake, kullum ana buƙatarsa domin rayuwa ba ta yiwuwa babu shi. Irin waɗannan mutane rahama ne a rayuwa. 2️⃣ Wani kamar numfashi yake, ana buƙatarsa a kowanne lokaci saboda muhimmancinsa da kusancinsa ga rayuwa. 3️⃣ Wani kamar magani yake, sai wasu lokuta ake buƙatarsa. Idan buƙata ta taso ne ake nemansa domin warware matsala. 4️⃣ Wani kuma kamar ciwo yake, ba a buƙatarsa a kowanne lokaci, domin kasancewarsa yana jawo damuwa da wahala. 5️⃣ Wani kamar cuta yake, kullum gudunsa ake yi, ana neman kariya da riga-kafi daga sharrinsa da cutarsa. 6️⃣ Wani kuma kamar sheɗan yake, ana neman tsari daga sharrinsa a kowanne lokaci saboda mugun tasirinsa da barna. Ya Allah Ka tsare mu daga mugun ji, mugun gani, mugun hali da mugayen mutane. Ka sa mu zama masu amfani ga al’umma, ba masu cutarwa ba .

All scholars

Now playing · Lesson

0:000:00

Almuhajir is on your phone

Follow scholars, save lessons, ask questions and download for offline listening in the Almuhajir app.

Coming soonApp StoreComing soonGoogle Play

Get the app